Yan Sanda a Jamus na tsare da wani makusancin Yahya Jammeh

Yahya Jammeh a lokacin da yake ficewa daga Gambia watan janairu 2015
Yahya Jammeh a lokacin da yake ficewa daga Gambia watan janairu 2015 REUTERS/Thierry Gouegnon

Mahukunta a kasar Jamus na tsare da wani dan asalin kasar Gambia, da suke zargin cewa yana daya ne daga cikin jami’an wata rundunar jami’an tsaro ta musamman da ke kashe abokan hamayya a lokacin mulkin tsohon shugaba Yahya Jammeh.

Talla

Mahukuntan Jamus sun bayyana sunan wanda ake zargin a matsayin Bai L.. wanda aka ce shi ne ya tuka motar da ke dauke da jami’an tsaron wannan runduna tsakanin watan disambar 2003 zuwa 2006, inda suka rika kashe masu hamayya da shugaba Jammeh.

Kungiyoyin kare hakkin Bil Adama sun zargi tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh da bai wa wata runduna da ke karkashin sa umarnin kashe wasu baki yan kasashen Afirka ta Yamma 50 a shekarar 2005.

Kungiyar Human Rights Watch da TRIAL International sun ce sun yiwa wasu tsoffin jami’an gwamnatin Gambia 30 tambayoyi akai, cikin su harda sojoji 11 da kuma wani da ya tsallake rijiya da baya daga harin, kuma sun tabbatar mata da kisan.

44 daga cikin bakin sun fito ne daga Ghana da Najeriya da Senegal da kuma Togo, wadanda ke neman zuwa Turai ta teku.

Kungiyoyin sun ce an kama su ne a gabar ruwan Banjul inda aka mika su ga rundunar da ke karkashin shugaban wadda ta hallaka su.

Wani bincike da kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS da Majalisar Dinkin Duniya suka gudanar a shekarar 2009 ya tababtar da cewar rundunar da ake zargin ce ta kashe su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.