Tanzania - John Magufuli

Shugaban Tanzania John Magufuli ya mutu

Tsohon shugaban Tanzania John Magufuli.
Tsohon shugaban Tanzania John Magufuli. AP - Khalfan Said

Shugaban Tanzania Johon Magafuli, ya mutu yana da shekaru 61 a duniya bayan share tsawon kwanaki ana rade-raden cewa yana fama da rashin lafiya.

Talla

Mataimakiyar shugaban kasar Samia Suluhu Hassan wadda tabbatar da wannan labari, ta ce Magafuli ya mutu ne sakamakon fama da ciwon zuwa.

Samia ta ce ranar 17 ga watan Maris na shekarar 2021 da misalin karshe 6 na yamma, shugaba John Pombe Joseph Magafuli ya rasu a asibitin Mzena da ke birnin Dares Salaam.

Tsohon shugaban kasar Tanzania, marigayi John Magufuli.
Tsohon shugaban kasar Tanzania, marigayi John Magufuli. AP - Stringer

Da farko dai an kwantar da shugaban ne ranar 6 ga watan Maris a asibitin Jakaya Kikwete don ba shi kulawa sakamakon rashin lafiyar ta ciwon zuciya da yake fama da shi kimanin shekaru 10.

Tuni aka fara shirye-shiryen jana’izar marigayin, tare da ware kwanaki 14 domin zaman makoki a duk fadin kasar, bayan sauko da tutar kasar zuwa kasa.

Daga cikin abubuwan da za a rika tuna marigayi John Magufuli shugaban Tanzania na 5, akwai aiki tukuru da yayi wajen samawa al’ummarsa kayayyakin more rayuwa abinda ya sa ake kiransa da sunan ‘Bulldozer’ wato Sarkin aiki.

Marigayi John Magufuli.
Marigayi John Magufuli. AP - Khalfan Said

Marigayi Magufuli ya kuma raba albashinsa gida 4 inda yake daukar kashi 1.

Batu na baya bayan nan kuma da za a rika tuna tsohon shugaban na Tanzania da shi, shi ne yin watsi da wanzuwar annobar Korona, bayan da ya ce binciken sirrin da ya sanya aka yi, ya gano cewar Akuya, man fetur da kuma gwanda sun kamu da cutar, dan haka akwai lauje cikin nadi dangane da barkewar annobar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.