An gudanar da zanga-zanga a biranen DR Congo kan kashe kashen 'Yan bindiga

Wasu daga cikin mutanen yankin Kivu yayin jana'izzar wasu mutane da aka kashe a yankin.
Wasu daga cikin mutanen yankin Kivu yayin jana'izzar wasu mutane da aka kashe a yankin. AFP

Harakokin yau da kullum sun tsaya cik a birane guda 3 dake Gabashin Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sakamakon zanga zangar da jama’a suka fita domin nuna bacin ran su da yadda wata kungiyar 'Yan bindiga ke kashe jama’a.

Talla

Masu zanga zangar sun durkusar da harakokin jama’a a biranen Beni da Oicha da kuma Butembo dake Arewacin Kivu sakamakon amsa kiran masu shirya zanga zangar a karkashin kungiyar Veranda Mutchanga.

Tsakiyar birnin  Butembo, dake arewacin kivu.
Tsakiyar birnin Butembo, dake arewacin kivu. Wikimedia/Creative Commons CC by Glooh at English Wikipedia

A birnin Beni an rufe shaguna da makarantu, yayin da jama’a suka kauracewa titunan garin, abinda ya baiwa fusatattun matasa damar sanya shinge akan hanyoyin mota, kafin daga bisani Yan Sanda su kawar da su.

A garin Oicha wanda shine mafi girma a Yankin Beni, Magajin Garin Nicolas Kikuku yace an kashe mai zanga zanga guda sakamakon harbin bindiga, yayin da wasu guda biyu suka samu raunuka.

An dai samu harbin bindigar ne lokacin da jami’an Yan Sandan kwantar da tarzoma ke kokarin kauda wani shinge da aka aje akan hanya.

Rahotanni sun kuma ce harkokin yau da kullum sun tsaya cik a Butembo, birnin Kasuwanci dake dauke da mutane sama da miliyan guda.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.