Tanzania

Samia Suluhu Hassan ta sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugabar Tanzania

Samia Suluhu Hassan, sabuwar shugabar kasar Tanzania.
Samia Suluhu Hassan, sabuwar shugabar kasar Tanzania. AP

Samia Suluhu Hassan ta sha rantsuwar kama aiki a matsayin sabuwar shugabar kasar Tanzania, nadin da ke zuwa bayan mutuwar shugaba John Magufuli a Larabar da ta gabata.

Talla

Shugaba Samia Suluhu Hassan mai shekaru 61 wadda tsohuwar mataimakiyar shugaba Magufuli ce za ta jagoranci kasar ta Tanzania zuwa 2025 ita ce shugaba mace ta farko da kasar ta gani a tarihi, kuma shugaba ta 6 bayan samun mulkin kasar.

An haife Samia Hassan a ranar 27 ga watan janairun 1960 a Zanzibar, inda ta yi karatu a matakai daban-daban na jami’oi kama daga na ciki da kuma wajen kasar, yayinda ta ke da kwarewa a fannin tattalin arziki.

Shugaba Samia ta shiga harkokin siyasa a shekarar 2000,  inda ta fara da rike mukamin ‘yar majalisa mai wakiltar Zanzibar gabanin shugaba Amani Karume ya nada mukamin ministar a 2005.

A shekarar 2010, ta lashe kashi 80 na kuri’un da aka kada a zaben ‘yan majalisun yanki, gabanin bata mukamin karamar ministar cikin gida a 2014.

A shekarar 2015, shugaba Magufuli, ya zabi Samia Hassan a matsayin wadda zai takara da ita.

Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi aure a 1978 tana da yara 4 ciki har da Mwanu Hafidh Ameir da ke amtsayin ‘yar Majalisa a yanzu.

Baya ga kasancewarta mace ta farko da ta hau kujerar shugabancin Tanzania ita ce musulma ta 3 da za ta jagoranci kasar bayan Ali Hassan Mwinyi da kuma Karume.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.