Chadi

Yan Sanda sun tarwatsa masu zanga zanga a Chadi

Wasu daga cikin jagororin yan Adawan Chadi  Saleh Kebzabo da Ngarlejy Yorongar yayin wani taron su a Djamena
Wasu daga cikin jagororin yan Adawan Chadi Saleh Kebzabo da Ngarlejy Yorongar yayin wani taron su a Djamena AFP - GAEL COGNE

Yan Sanda a kasar Chadi yau sun tarwatsa masu zanga zanga daga Yan adawa zuwa kungiyoyin fararen hula domin nuna adawar su da sake takarar shugaba Idris Deby a zaben da za’ayi a watan gobe.

Talla

Rahotanni sun ce masu zanga zangar basu fito da yawa ba saboda girke tarin jami’an tsaro bayan da gwamnatin kasar at sanar da haramta zanga zangar saboda fargabar tada hankali.

Daga cikin wadanda suka shiga zanga zangar ta yau harda Success Masra, daya daga cikin mutanen da kotun koli ta haramtawa tsayawa takarar zaben.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun hana babban dan adawa Saleh Kebzabo isa wurin da aka shirya zanga zangar, yayin da aka kama Mahamat Nour Ahmed Ibedou, Sakataren kungiyar kare hakkin Bil Adama ta CTDDH. 

Shaidun gani da ido sun ce Yan Sanda sun yi kawanya ga cibiyar Jam’iyyar Masra, yayin da suka kuma tarwatsa wadanda suka kona tayun mota a sassan birnin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.