Tanzania

An Yi Bukin Binne Gawan Marigayi Shugaba John Magufuli Na Tanzania

Gawar Marigayi John Magufuli a lokacin da ake yi mata adduoi kafin a binne ta.
Gawar Marigayi John Magufuli a lokacin da ake yi mata adduoi kafin a binne ta. REUTERS - STRINGER

Shugabannin kasashen Africa sun yi  juyayi sosai saboda mutuwar marigayi John Magufuli  na Tanzaniya wanda aka binne shi yau Littini bayan mutuwarsa makon jiya sakamakon rashin lafiya da babu wanda ya san irinta.

Talla

Dubban mutane suka halarci binne gawan bayan baje kolin ta da aka yi a filin wasanni dake birnin Dodoma.

Wasu sun yi ta rusa kuka, wasu har suma suka yi a bukin binne gawan da aka yi wanda wasu shugabannin Afrika da wasu baki daga kasashen waje suka halarta.

Wasu daga cikin shugabannin kasashen da suka halarci bukin ba su sanya takunkumin rufe fuska ba kamar yadda ake bukata don hana yaduwar cutar Coronavirus.

Marigayi shugaba John Magufuli mai shekaru 61 ya kwashe makonni uku ba’a ganin sa a bainin jama’a kafin samun labarin mutuwarsa makon jiya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.