Kamaru-Boko Haram

Mutane 3 sun mutu a wani harin da 'mayakan Boko Haram suka kai Kamaru

Arewacin Kamaru na fama da hare-haren 'yan ta'adda da ke shigowa daga Najeriya.
Arewacin Kamaru na fama da hare-haren 'yan ta'adda da ke shigowa daga Najeriya. AFP/File

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai hari wani kauyen da ke Jihar Arewa mai nisa a kasar Kamaru, abin da ya yi sanadiyar kashe mutane 3, cikin su har da mata biyu.

Talla

Wani kansilar dake wakilatar yankin yace an kai harin ne a kauyen Bla-Goussi Torou dake kan iyakar Najeriya da kasar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wani hari da boko haram ta kai garin Wulgo dake Najeriya yayi sanadiyar kashe sojojin Kamaru guda 2.

Ayyukan kungiyar Boko Haram da ke ikirarin jihadi a arewa maso gabashin Najeriya sun girgiza ilahirin yankin, har ma su na shafar kasashen da ke makwaftaka da ita.

Chadi, Kamaru da Nijar sun sha fama da hare-haren kungiyar Boko Haram da ke shigowa da Najeriya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI