Congo Brazzaville-Zabe

Shugaba Nguesso ya sake lashe zaben Congo Brazziville da kashi 88.57

Shugaba Denis Sassou-Nguesso, bayan nasararsa ta alshe zaben kasar da gagarumin rinjaye.
Shugaba Denis Sassou-Nguesso, bayan nasararsa ta alshe zaben kasar da gagarumin rinjaye. AP - Kamil Zihnioglu

Shugaba Denis Sassou Nguesso ya sake lashe zaben kasar Congo Brazziville da rinjaye kasha 88.57 na yawan kuri’un da aka kada kamar yadda alkaluman hukumar zaben kasar ke nunawa.

Talla

Sassou Nguesso mai shekaru 77 tsawon shekaru 36 kenan yana mulkin Congo tun bayan darewarsa Mulkin kasar a shekarar 1979.

Gagarumar nasarar shugaban wadda ministan cikin gida na kasar ya sanar bata zowa al’umma da mamaki musamman bayan janyewar babbar jam’iyyar adawa a zaben kuma mutuwar dan takara daya tilo da ke karawa da Nguesso a zaben wato, Guy-Brice Parfait Kolelas da coronavirus ta kasha yana da shekaru 61.

Sai dai duk haka mataccen dan takarar ya samu kasha 7.84 na yawan kuri’un da aka kada.

Masu sanya ido kan zaben na Congo Brazziville sun ce kasha 67.55 na yawan masu takardun zabe ne kadai suka kada juri’a a zaben, dai dai lokacin da shugaban guda cikin mafiya dadewa a karagar Mulki ke fama da matsin lamba daga bangaren adawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.