Congo

Sojin Jamhuriyyar Congo sun hallaka 'yan tawayen kasar 27 a wani farmaki

Tawagar 'yan tawayen Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.
Tawagar 'yan tawayen Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo. Reuters/James Akena

Rundunar Sojin Jamhuriyar dimokiradiyar Congo ta sanar da murkushe 'yan tawayen da suka addabi jama’ar kasar 27, yayin da wasu fararen hula 5 da soja guda suka mutu sakamakon hare haren da suka kaddamar domin kawar da masu dauke da makamai dake gabashin kasar.

Talla

Kakakin sojin kasar Lafatanar Jules Ngongo yace daga cikin mutane 27 da aka kashe daga kungiyar Yan Tawayen ta CODECO akwai daya daga cikin mayan kwamandodin su.

Ita dai kungiyar CODECO da ta kunshi kungiyoyin Yan bindigar dake nasaba da siyasa da siyasa da kuma addini tayi sanadiyar hallaka akalla mutane sama da 1,000 a Congo tun daga watan Disambar shekarar 2017.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.