Nijar

Macron ya tattauna da zababben shugaban Jamhuriyar Nijar

Mohamed Bazoum zababben shugaban Jamhuriyar Nijar a yayin ganawa da Shugaban Faransa
Mohamed Bazoum zababben shugaban Jamhuriyar Nijar a yayin ganawa da Shugaban Faransa © AFP - Fethi Belaid

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tattauna da zababben shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed daga fadarsa  da ke Paris inda ya yabawa 'Yan Nijar kan rawar da suka taka wajen ganin an samu mika mulki cikin kwanciyar hankali.

Talla

Shugaba Macron ya mikawa Bazoum fatar alherin mutanen Faransa tare da Majalisar dokokin Nijar da aka kaddamar, yayin da yayi Allah wadai da kazamin harin ta’addancin da aka samu a kasar wanda yayi sanadiyar kashe mutane 137 a Tahoua.

Motar jami'an zaben Jamhuriyar Nijar da ta taka nakiya a yankin Tillaberi
Motar jami'an zaben Jamhuriyar Nijar da ta taka nakiya a yankin Tillaberi RFI Hausa/ Salisu Issa

Shugabannin biyu sun bayyana aniyar su ta aiki tare wajen yaki da 'Yan ta’adda kamar yadda yarjejeniyar taron kungiyar G5 Sahel ya amince a taron da akayi a N’Djamena ranar 15 ga watan jiya.

Fadar shugaban Faransa tace Macron ya sha alwashin baiwa zababben shugaban kasar Nijar cikaken taimako domin cigaba da shirin Nijar na inganta ilimin yara mata.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.