An dage zaben kananan hukumomi a Senegal
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Gwamnatin Senegal ta sanar da sake jingine zabukan kananan hukumomin kasar da aka shirya gudanarwa a wannan wata, wanda shine karo na uku da ake jingine wannan zabe wanda aka tsara gudanarwa a shekara ta 2019.
Babu dai sabon ranar da aka tsaida don wannan zabe, kuma kamar yadda wata sanarwar gwamnati ke cewa wadanda suke rike da kujerun ne aka umarci su zarce da mulkin.
Kusan mako daya kenan da yan adawa suka shirya gaggarumar zanga-zanga don nuna bacin ran su biyo bayan kamu daya daga cikin jagoran su.Sai dai daga baya jam'iyyun adawar kasar sun sanar da dage wannan zanga-zanga.
‘Yan adawar kasar Senegal sun sanar da dakatar da zanga zangar da suka kira sakamakon kama Ousmane Sonko da aka yi, abinda ya haifar da mummunar arangama da kuma mutuwar mutane akalla 5 a kasar.
Shugaba Macky Sall wanda jam'iyarsa ke mulkin yawancin kananan hukumomin kasar, ya kaddamar da tattaunawar makomar kasar tun a watan Mayu, na shekara ta 2019 tsakanin mutan kasar da niyyar warware rikicin siyasar kasar ta Senegal.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu