Chadi

Kotu ta sallami babban sakataren hadin guiwar kungiyoyin kare dan Adam a Chadi

Babban sakataren hadin guiwar kungiyoyin kare hakkin dan Adam ta kasar chadi Mahamat Nour Ibedu
Babban sakataren hadin guiwar kungiyoyin kare hakkin dan Adam ta kasar chadi Mahamat Nour Ibedu © Ali Younouss Ali

A jiya laraba kotu ta sallami babban sakataren hadin guiwar kungiyoyin kare hakkin dan Adam ta kasar Chadi Mahamat Nour Ibedu bayan share tsawon kwanaki 3 a tsare a wata cibiyar yan sanda dake Ndjamena.

Talla

Shugabanin yan siyasa a kasar ta Chadi tareda hadin gwuiwar kungiyoyin farraren hula ke ci gaba da adawa da yunkurin Shugaban kasar Idriss Deby Itno na sake tsayawa takara.

Shugaban Chadi,Idriss Deby kuma dan takara a zaben wannan kasa.
Shugaban Chadi,Idriss Deby kuma dan takara a zaben wannan kasa. POOL/AFP/File

Hukumomion kasar sun baiwa jami’an tsaro umurni na murkushe duk wata zanga-zanga da kan iya kuno kai a wasu biranen kasar ta Chadi.

An dai kama dan gwagwarmayar kare hakkin dan Adam din ne a ranar assabar 20 ga wanan wata na Maris a cikin wata zanga zangar nuna kin amincewa da takarar shugaba 'Idriss Deby a wani sabon wa’addin shugabanci kasa na 6. Zanga zangar da aka haramta.Ga abinda Mahamat Nour Ibedu ke cewa yan lokuta da sako shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.