Mali-Faransa

Al'ummar Mali na zanga-zangar bukatar ficewar Sojin Faransa daga kasar

Bukatar ficewar Sojin na Faransa daga Mali ya biyo bayan kisan wasu matasa 6 da Sojin Faransar suka yi a Daji yayin farmaki kan mayaka masu ikirarin jihadi.
Bukatar ficewar Sojin na Faransa daga Mali ya biyo bayan kisan wasu matasa 6 da Sojin Faransar suka yi a Daji yayin farmaki kan mayaka masu ikirarin jihadi. AFP/File

Wasu Mutane yau sun gudanar da zanga zanga a Bamako da ke kasar Mali inda su ke bukatar ganin sojojin Faransa sun fice daga kasar mai fama da tashe-tashen hakula, kwana guda bayan mutuwar mutane 6 sakamakon harin sojojin Faransar.

Talla

Rundunar sojin Faransa ta ce ta kai harin ne kan masu fafutukar jihadi a arewa maso gabashin Mali, amma mazauna yankin sun ce matasa ne da ke farauta aka kashe.

Kasar Faransa ta kai wa Mali dauki a shekarar 2013 domin taimakawa gwamnatin kasar kawar da masu fafutukar kafa daula a yankin.

Yanzu haka Faransa na da dakaru 5,100 a yankin Sahel dake aiki a karkashin rundunar Barkhane.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.