Tattalin arziki-Dangote

Aliko Dangote ya ci gaba da zama mafi kudi a Attajiran nahiyar Afrika

Fitaccen attajirin Nahiyar Afrika Aliko Dangote.
Fitaccen attajirin Nahiyar Afrika Aliko Dangote. REUTERS/Denis Balibouse

Fitaccen Attajirin Nahiyar Afrika Aliko Dangote ya ci gaba da zama wanda ya fi kowa arziki a nahiyar cikin wani sabon rahoton mujallar Insider Monkey kan jerin mutane 15 da suka fi kowa arziki a Afrikan, Attajiran da ake ganin za su taka gagarumar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin nahiyar.

Talla

Binciken da Mujallar Insider Monkey ta wallafa ya yi tsokaci kan dukiyar da attajiran suka mallaka da kuma harkokin kasuwancin da su ke yi.

Ga sunayen 10 daga cikin attajiran 15 da kuma yawan dukiyar da suka mallaka.

1 – Aliko Dangote – Najeriya - Shekaru 63 – Ya mallaki dukiyar da ta kai Dala biliyan 11 da miliyan 300 abinda ya sa ya zama mutumin da yafi kowa dukiya a nahiyar Afirka. Dangote ya mallaki kamfanoni da dama da suka hada da na siminti da kayan abinci da lemu da takin zamani da kuma matatar fetur da ake saran fara aikin ta nan bada dadewa ba.

2 Nassef Sawiris - Masar – Shekaru 59 – Ya mallaki dukiyar da ta kai Dala biliyan 8 da miliyan 120. Kamar ‘yan uwan sa Naguib da Samih, Nassef na daga cikin attajiran Afirka. Shine shugaban kamfanin gine ginen Orascom wanda daga baya ya rabe. Yana da kashi 6 na hannun jari a kamfanin sarrafa kayan wasannin Adidas kuma yanzu haka shi ya mallaki kamfanin kwallon kafar Aston Villa dake Ingila.

3 Nicky Oppenheimer – Afirka ta Kudu  –  Shekaru 75 – Ya mallaki dukiyar da ta kai Dala biliyan 8. Oppenheimer ya fito ne daga gidan masu hannu da shuni da suka yi fice a harkokin kasuwancin Afirka ta kudu. Daga cikin ayyukan su harda hakar lu’u lu’u da kakannin sa da iyayen sa suka yi, harkar da ya gada, yayi kuma fice akai. Shine shugaban kamfanin hakar lu’u lu’u na DeBeers da kamfanin kasuwancin Anglo-Americans dake yake da jarin kashi 85, yayin da Gwamnatin Botswana ke da kashi 15. Oppenheimer ne attajirin da yafi kowa dukiya a Afirka ta kudu ayau.

4 Johann Rupert – Afirka ta kudu – Shekaru 70  – Ya mallaki dukiyar da ta kai Dala biliyan 7 da miliyan 300. Ya mallaki kamfanin Richemont dake sayar da kayan sawa da kuma agoguna da kayan kawa.

5 Mike Adunuga – Najeriya – Shekaru 65 – Ya mallaki dukiyar da ta kai Dala biliyan 6 da miliyan 100. Adenuga ya samu kudi ne ta hanyar kamfanin sadarwar sa ta Globacom, wanda shine kamfanin sadarwa na biyu mafi girma a Najeriya wanda ke da mutane miliyan 43 dake amfani da kayukan sa. Adenuga na da hannayen jari a kamfanin man Conoil da Bankin Equatorial Trust Bank, abinda ya bashi damar zama mutumi na biyu mafi kudi a Najeriya bayan Aliko Dangote.

6 - Abdulsamad Rabiu - Najeriya – Shekaru 60 – Dala biliyan 5 da rabi. Ya mallaki kamfanin BUA wanda ya kunshi masana’antu da gine gine da kuma noma. Kuma yanzu haka yana kokarin gina kamfanin tace man fetur.

7 – Issad Rebrad - Algeria – Shekaru 77 – Ya mallaki Dala biliyan 4 da miliyan 800. Ya mallaki kamfanin samar da abinci da hada motoci da kayan gida da harkokin sufurin kasa da na ruwa da harkokin karafa. Ya kuma mallaki kamfanoni da dama a Turai da Afirka da Kudancin Amurka.

8 - Naguib Sawiris – Masar – Shekaru 66 – Ya mallaki Dala biliyan 3 da miliyan 200. Sawiris ya fito ne daga gidan attajiran masar kuma shine shugaban kamfanin sadarwar Orascom. A karkashin jagorancin sa kamfanin ya samu gagarumin cigaba wajen bude rassan sa a wasu kasashen Afirka. Kamfanin sa na sadarwa shine na 6 mafi girma a duniya inda yake aiki a kasashe 20 da kuma masu amfani da layukan sa miliyan 181.

9 – Patrice Motsepe – Afirka ta kudu - Shekaru 58 – Ya mallaki dukiyar da ta kai Dala biliyan 3. Ya zamu kudin sa ne ta hanyar hakar ma’adinai. Ya fara rayuwa a matsayin lauya kafin daga bisani ya kafa kamfanin Africa Rainbow domin hakar ma’adinan da suka hada da zinare da karafa, kuam yanzu haka yana jagorancin kamfanoni da dama a Afirka. Yanzu haka shine shugaban Hukumar kwalon kafar Afirka.

10 – Koos Becker – South Africa – Shekaru 68 – Ya mallaki dukiyar da ta kai Dala biliyan 2 da miliyan 800. Becker ne shugaban gungun kamfanonin yada labaran Naspers wanda ke da cibiyoyi a China da Amurka da kuma India. Kamfanin na daga cikin wadanda ke tallata hanayen jarin sa a kasuwannin hannayen jarin Johannesburg da London. Becker ya zuba jari a kamfanon sadarwar da dama cikin su harda manyan kafofin yada labaari irin su DSTV da OXL da kuma MTN.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.