Najeriya-Morocco

Najeriya da morocco sun sanya hannu kan yarjejeniyar kafa kamfanin takin zamani

Samar da takin zamanin zai taimakawa kasashen biyu bunkasa harkokinsu na Noma.
Samar da takin zamanin zai taimakawa kasashen biyu bunkasa harkokinsu na Noma. © AFP - Rijasolo

Najeriya da Kasar Morocco sun sanya hannu kan wani kuduri na kafa kamfanin samar da takin zamani na kudi har Dalar Amurka biliyan 1.3,  a wani yunkuri da kasashen biyu ke yi na samar da taki ga manomansu cikin sauki da kuma kara bunkasar cinikayya a tsakaninsu. Daga Abuja, ga rahoton Muhammad Kabir Yusuf.