RFI

RFI na goyan bayan wakilinta Pierre Firtion -Sanarwa

Sanarwar goyan baya daga Rfi sashen Faransanci
Sanarwar goyan baya daga Rfi sashen Faransanci © RFI

A daidai lokacin da wasu kafofin yada labaran kasar Togo ke dada bayar da  labaran  karya kan dan jaridan rediyon Faransa sashen Faransanci, reshen Afrika, wato Pierre Firtion, magabatan gidan rediyon Faransa na RFI a wata sanarwa da suka fitar a jiya Juma’a sun tabbatar da cewa babu wani hukunci ko mataki da suka dauka  a kan wannan dan jarida , da ke da kwarewa da sanin makaman aiki.

Talla

Pierre Firtion da ke aiki a matsayin wakili a sashen Faransanci  na RFI reshen Afrika ya rubuta wani labari a ranar 31 ga watan Maris ta shekara ta 2020 inda ya ke cewa Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya aike da wasika ga Shugaban Togo,

sanarwar goyan baya ga dan jarida Reporter Pierrre Firtion na Rfi
sanarwar goyan baya ga dan jarida Reporter Pierrre Firtion na Rfi © RFI

RFI ta tabbatar da haka cewar tabbas Shugaba Macron ya rubbuta wannan wasika. Kawo wannan labari daga wannan wakili ya janyo masa suka da barrazana, wanda RFI ta ce ba za ta hanna shi gudanar da aikinsa ba, saboda haka RFI na bayyana  goyon baya 100 bisa dari tare da kasancewa da shi a  hukumance  ta bangaren shari’a.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.