Afrika

Turkiya na shirin ceto jirgin ruwan Masar Ever Given a mashigin canal de Suez

Jirgin ruwan Masar Ever Given a mashigin Canal de Suez
Jirgin ruwan Masar Ever Given a mashigin Canal de Suez . Suez CANAL/AFP

A kokarin Turkiya na sake dawowa da hulda da Masar,hukumomin Ankara sun shawarci  kasar da shirin sun a aikewa da wani jirgin  da zai taimaka  wajen janye jirgin Masar mai suna Ever Given da ya toshe mashigin ruwan Canal de Suez,wanda ya kuma janyo cikonso jirage da dama yanzu haka.

Talla

Tsawon shekaru takwas kenan da Masar da Turkiya ke zaman doya da man ja,sai dai kusan makonni biyu kenan da Turkiyya ke ta kokarin shawo kan hukumomin Masar don ganin sun koma kawayen juna.

Tun a shekara ta 2013 ne kasashen biyu suka raba garin ,sanadiyyar kifar da gwamnatin Mohamed Morsi dake karkashin inuwar ‘yan uwa Musulmi.

Tun wancan lokaci Turkiya ta yi watsi da Masar tareda danganta sabuwar gwamnatin Masar da haramtata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.