Najeriya-Boko Haram

Dalilin da ya sa rundunar hadin kai bata nasara - Deby

Idriss Déby Itno, Shugaban kasar Chadi
Idriss Déby Itno, Shugaban kasar Chadi RFI

Shugaban kasar Chadi Marshall Idris Deby ya bayyana abinda ya kira dalilan da suka sa rundunar sojin hadin kai ta kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi bata samun nasara a yakin da take wajen murkushe mayakan boko haram.

Talla

Yayin da yake tsokaci bayan ganawar da yayi da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Abuja, Deby wanda ya bayyana fatar sa na ganin sojojin sun samu nasara kan 'Yan ta’addan yace rashin kai musu hari akai akai shi ke haifar da matsala wajen yakin.

 

Deby yace ayyukan ta‘addanci na cigaba da zama babban batu a Yankin Tafkin Chadi da kuma kasashen Sahel saboda rundunar hadin gwuiwar bata kai hare hare lokaci zuwa lokaci.

Marshall Deby yace ya tattauna batun da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari inda ya shaida masa cewar kai hari sau guda da rundunar keyi a shekara ba zai bada damar samun nasara akan yan ta’addan ba.

Muhammadu Buhari da  Idriss Deby
Muhammadu Buhari da Idriss Deby Pulse

Shugaban Chadin ya bayyana fatar sa cewar sabbin dabarun yakin da aka kaddamar da kuma sauyin shugabannin da aka samu zasu taimaka wajen gabatar da sabbin dabarun da za’a samu nasara akai.

Deby ya kuma ce bayan yaki da yan ta’adda, sun kuma tattauna batutuwan da suka shafi kasashen Najeriya da Chadi tare da shugaba Buhari.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.