Mozambique-Ta'addanci

Masu ikirarin jihadi a Mozambique sun karbe ikon garin Palma

Taswirar kasar Mozambique da ke nuna lardin Cabo Delgado
Taswirar kasar Mozambique da ke nuna lardin Cabo Delgado Kun TIAN AFP

Mayaka masu ikirarin jihadi a Mozambique sun karbe iko da wani gari da ke arewacin kasar, inda suka kashe mutane da dama cikinsu har da wani ma’aikaci guda daga kasar waje, lamarin da ya tilasta wa kamfanin mai na kasar Faransa, wato Total dakatar da gagarumin aikin bututun iskar gasa da ya ke yi a yankin.

Talla

Mayakan sun fara kai farmaki ne a lardin Cabo Delgado da ke arewacin kasar a ranar Laraba, abi da ya sa a la tilas aka kwashe mutane 200 daga wani otel, cikin su har da ma’aikata daga kasashen waje da ke aikin bututun iskar gas.

Harin na zuwa ne jim kadan bayn da kamfanin Total ya sanar da cewa a sannu a hankali zai koma aiki ka’in da na’in a yankin, bayan ‘yar dakatarwa sakamkon yawaitar hare-hare.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.