Coronavirus-Afrika

Masu corona a Afrika sun zarce miliyan 14

Sama da mutane miliyan 14 suka harbu da kwayar cutar coronavirus a nahiyar Afrika kamar yadda Hukumar Yaki da Cutuka masu Yaduwa ta Nahiyar ta sanar
Sama da mutane miliyan 14 suka harbu da kwayar cutar coronavirus a nahiyar Afrika kamar yadda Hukumar Yaki da Cutuka masu Yaduwa ta Nahiyar ta sanar © ANNIE RISEMBERG/AFP

Hukumar da ke yaki da cututtuka ta Afirka ta ce adadin mutanen da suka kamu da cutar korona a fadin nahiyar sun kai miliyan 14 da dubu 187,097, yayin da dubu 111 da 919 suka mutu, yayin da miliyan 3 da dubu 746 da 992 suka warke.

Talla

Hukumar ta bayyana kasashen Afirka ta Kudu da Morocco da Tunisa da Masar da kuma Habasha a matsayin wadanda suka fi jin radadin cutar.

Idan aka koma batun shiya-shiya kuma, shiyar kudancin Afirka ke sahun gaba, sai Afirka ta arewa da gabashin Afirka, yayin da cutar ke da sauki a yankin tsakiyar nahiyar.

Ya zuwa yanzu kasashen Afirka sun karbi allurar rigakafin cutar sama da miliyan 26 a karkashin shirin taimaka musu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.