Afrika ta kudu ta haramta sayar da giya lokacin Easter

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa
Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa POOL/AFP/Archivos

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana haramta sayar da giya na kwanaki 4 lokacin bikin Easter domin dakile yaduwar cutar korona.

Talla

Yayin jawabi ga al’ummar kasar, shugaban yace sun gano cewar mutanen da suka kwankwadi giyar na aikata laifuffukan da basu dace wadanda ke yada cutar, saboda haka daga ranar juma’a ba za’a sayarwa mutane giyar su kai gida ba har zuwa ranar litinin.

Shugaban Kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa kuma shugaban kungiyar tarayyar Afrika AU.
Shugaban Kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa kuma shugaban kungiyar tarayyar Afrika AU. REUTERS/Sumaya Hisham/File Photo

Sai dai yace za’a bar ta ga masu sha a gidajen abinci da gidan giyar.

Mutane sama da miliyan guda da rabi suka kamu da cutar korona a kasar, kuma 52,700 daga cikin su sun mutu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.