Masar

Masar ta kame mutum 8 da ke da hannu a haddasa hadarin jirgin kasa

Hadarin jirgin kasan Masar da ya hallaka tarin jama'a.
Hadarin jirgin kasan Masar da ya hallaka tarin jama'a. - AFP

Kasar Masar ta sanar da kame wasu mutane 8 da ake zargi da hannu a haddasa hadarin jirgin kasan da ya hallaka tarin jama’a a makon jiya bayan da jirage biyu suka yi taho mu gama, matakin da ke zuwa dai dai lokacin da ma’aikatar lafiya ke sanar da raguwar alkaluman mutanen da suka mutu a hadarin zuwa 18 maimakon 32 da aka sanar a baya.

Talla

Masu shigar da kara a Masar sun yi umarnin ci gaba da tsare mutanen da suka hada da matukan jirgin biyu, mataimakansu da kuma jami’in da ke kula da sashen bayar da umarnin wucewar jiragen, da kuma wasu jami’ai biyu wadanda aka zarga da sakaci a afkuwar hadarin wanda ya jikkata karin mutane 200.

Matakin ya biyo bayan shan alwashin da shugaba Abdel Fattah al-Sisi ya yi na hukunta duk wadanda suke da hannu a hadarin mafi muni da kasar ta gani a baya-bayan nan.

Tun a wancan lokacin hukumar kula da jiragen kasa ta Masar ta ce, wasu fasinjojin da ba asan ko su wanene ba suka haddasa hadarin bayanda su ka yi ta yunkurin tsayar da jirgin ta hanyar janyo waigi ko kuma igiyar tsayar da jirgin na gaggawa wanda ya haddasa matsala ga birki da ya kai ga karkacewarsa daga layin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.