Qatar ta goyi bayan gagarumin shirin zuba jari a DR Congo

Shugaban kasar Congo Félix Tshisekedi.
Shugaban kasar Congo Félix Tshisekedi. Sumy Sadurni / AFP

Ofishin Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ya sanar da cewa, shugaban kasar Felix Tshisekedi da mai martaba sarkin Qatar Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani sun sanya hannu kan wata yarjejeniya kan wani gagarumin Shirin zuba jari daga Qatar.Sanarwar da fadar gwamnatin Dimokradiyar Congo ta fitar ta shafin Twitta, yau Talata tace, an kulla yarjejeniyar ce, bayan da shugaba Tshisekedi dake jagorantar kasa mafi girma a yankin Kudu da Saharar Afirka, ya gana da sarki Tamin Al-Thani a jiya Litinin. 

Talla

Sanawar tace, "An sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama, na fahimtar juna ... musamman ta fuskokin tattalin arziki, kasuwanci da fasaha da kuma hadin guiwa ta fannin jiragen sama da na ruwa." Matakin da zai kai ga zamanantar da filyen jiragen sama da na ruwa a jamhuriyar Congo.

Taswirar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo
Taswirar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo AFP

Allah ya albarkacin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da dumbin arzikin ma'adinai da albarkatun noma, da kuma Hada-hadar kasuwar kimanin mutane miliyan 86.

To sai dai, tana fama da tsananin talauci da rashin daidaito da kuma cin hanci da rashawa da kuma rashin shugabanci na gari.

Tshisekedi ya hau kan karagar mulki a watan Janairun shekarar 2019 bayan wanda ya gada, Joseph Kabila, ya sauka bayan kwashe tsawon shekaru 18,  wanda ya kai ga mika mulki cikin lumana na farko a tarihin kasar.

Ziyar Tshisekedi zuwa kasar Qatar ta gamu da suka daga wani sanannen mai goyon bayan Kabila – wato Barnabe Kikaya bin Karubi, tsohon mai ba da shawara kan harkokin diflomasiyya ga fadar shugaban kasa kuma a baya ya kasance jakadan London.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.