Tanzania

Shugabar Tanzania Suluhu Hassan ta nada ministan kudi Mpango a matsayin mataimakin ta

Suluhu Hassan, Shugabar kasar Tanzania
Suluhu Hassan, Shugabar kasar Tanzania AP

Shugabar Kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta zabi ministan kudi Philip Mpango a matsayin mataimakin ta, yayin da take kokarin kafa sabuwar gwamnati sakamakon rasuwar tsohon shugaban kasa John Magufuli.

Talla

Mpango tsohon malamin jami’a ne kuma tsohon babban jami’in tattalin arziki a Bankin Duniya, kuma ya shaidawa majalisar kasar aniyar sa ta taimakawa sabuwar shugabar kasar wajen aiwatar da manufofin gwamnati.

Suluhu Hassan Shugabar kasar Tanzania
Suluhu Hassan Shugabar kasar Tanzania © blog.ikulu.go.tz

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Yan Sandan kasar ke bayyana karuwar adadin mutanen da suka mutu sakamakon tirmitsitsin da aka samu wajen jana’izar tsohon shugaban kasar wanda yanzu haka ya kai mutane 45.

John Magufuli ya rasu ne yana da shekaru 61 a ranar 17 ga watan Maris sakamakon bugun zuciya kamar yadda hukumomin kasar suka sanar.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.