MDD-Libya

Antonio Guterres na son MDD ta aike da tawaga ta musamman Libya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. Michael Sohn POOL/AFP/Archivos

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bada shawarar aikewa da tawagar sa ido domin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar zaman Lafiyar Libya da aka kulla.

Talla

A rahotan da Sakataren ya rubutawa kwamitin sulhu ya bukaci amincewa da shirin aikewa da tawagar da kuma bayyana aikin da yan tawagar zasu yi wajen ganin an samu dawamammanen zaman lafiya a kasar.

A watan Oktobar bara bangarorin da ke rikici a Libya a karkashin jagorancin Janar Khalifa Haftar da bangaren gwamnatin rikon kwarya sun sanya hannu kan shirin tsagaita wuta wanda ya bada damar samar da sabuwar gwamnatin rikon kwaryar dake aiki a Libya yanzu haka.

Ana saran gwamnatin ta shirya zabe a cikin wannan shekarar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.