Kamaru-Boko Haram

Kamaru ta girke sojoji kan iyakar Najeriya don yaki da Boko Haram

Sojojin Kamaru masu yaki da ta'addanci.
Sojojin Kamaru masu yaki da ta'addanci. AFP/File

Hukumomin Kamaru sun bada sanarwar tura karin sojoji zuwa kan iyakar kasar da ke arewa da Najeriya bayan jerin hare-haren da suka ce kungiyar Boko Hara ke kai wa yankin.

Talla

Hukumomin na Kamaru sun dauki wannan mataki ne har ma da sanya karin mayakan sa kai daga kauyuka don mayar da martani,  duk da cewa kungiyar Boko Haram ba ta fito ta dauki alhakin hare-haren ba ake ta kai wa ba.

Mijinyawa Bakary, wanda shi ne gwamnan jihar arewa mai nisa na Jamhuriyar Kamaru  da ke iyaka da jihar Borno ta Najeriya, inda cibiyar kungiyar Boko Haram take,  ya ce fiye da mayakan kungiyar 100 ne suka kai farmaki wani sansanin sojin kasar da ke Dabanga a ranar Asabar da ta gabata.

Ya ce ‘yan ta’addan sun kashe sojan Kamaru guda, suka kuma raunata 2, yayin da sojojin suka kashe 20 daga cikinsu a martanin da suka mayar, suka kuma karbe babura 7 datarin makamai, sai dai an yi rashin sa’a fararen hula 2 har da mace mai juna 2 sun mutu a yayin da ake gumurzu da ‘yan ta’addan.

Tun daga ranar Asabar da lamarin ya auku, harkokin kasuwanci suka tsaya cik  a kauyen Dabanga  na jihar arewa mai nisa a Kamaru, a cewar wani mai kiwon shanu a gidan gona, Donald Kulbe, inda ya kara da cewa tun daga wannan rana ta Asabar, al’ummar kauyen da dama suka tsere zuwa dazuka don neman tsira.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI