Kamaru

‘Yan awaren Kamaru na kaiwa fararen hula hari

Yankin Bamenda na kasar Kamaru
Yankin Bamenda na kasar Kamaru AFP / Reinnier Kaze

Wani sabon rahoton majalisar dinkin duniya ya nuna cewar rikicin ‘yan awaren dake addabar yankin masu amfani da turancin Ingilishi a Kamaru na cigaba da shafar fararen hula, bayan sabunta kaiwa makarantu hare-hare, da kuma yiwa wadanda basu ji ba basu gani ba kisan gilla, a watannin baya bayan nan.

Talla

Majalisar dinkin duniyar ta ce hare-haren shi ne mafi muni a baya bayan nan da aka gani a yankin arewa maso yammaci da kuma kudu maso yammacin Kamaru, sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin ‘yan aware da jami’an tsaro, rikicin da ya raba mutane sama da dubu 700 da muhallansu a cikin kasar, yayin da karin wasu akalla dubu 63, 800 suka tsere zuwa Najeriya.

Wasu daga cikin yan gudun hijira da suka tsere daga Kamaru
Wasu daga cikin yan gudun hijira da suka tsere daga Kamaru ©

A cewar majalisar dinkin duniyar, rikicin ya shafi mutane miliyan uku cikin miliyan hudu dake yankin da ake amfani da turancin ingilishi.

Rikicin ya samo rafo ne tun shekarar 2016 lokacin da jami ;an sojoji a kasar suka yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen tarwatsa masu zanga-zanga yawancin su ma’aikatan shari’a da malaman makaranta da ken una fushin su kan wariyar da ake nunawa yankin.

Wannan ne kuma ya sa kungiyoyi samada 30 suka dauki makamai tareda tawaye ga gwamnatin kasar da kuma neman ballewa don samar da tasu Kasarda suka yiwa take da Ambazonia.Haka kuma wata kungiya da ta ayyana kanta a matsayin gwamnatin sabuwar Ambazonia tare da bayyana aniyar ta na jagorantar yankin daake amfani da turancin ingilishi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.