Chadi - Nijar

Chadi ta kame sojojinta da ake zargi da lalata da mata a Nijar

Sojijin Chadi dake taimakawa kasahen yankin tafkin Chadi wajen yaki da Boko Hram
Sojijin Chadi dake taimakawa kasahen yankin tafkin Chadi wajen yaki da Boko Hram AFP

Gwamnatin Chadi ta sanar da tsare wasu sojojinta da ake zargi da yi wa mata aƙalla uku fyaɗe a jamhuriyar Nijar, ko da yake bata bayyana adadin sojojin ba.

Talla

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito ma’aikatar harakokin wajen ƙasar ta Chadi na cewa za a hukunta jami’an bisa laifin da suka aikata da kuma neman ɓata sunan sojin ƙasar.

A ranar Juma’ar da ta gabata  hukumar kare haƙƙin bil’adama ta Nijar ta buƙaci gudanar da bincike kan zargin da ake yiwa sojojin Chadi na yiwa wasu mata fyade, ciki har da wata yarinya mai shekaru 11.

Dakarun Chadin da ake zargin na Jamhuriyar Nijar ne inda suke taimakawa wajen yaki da ‘yan ta’adda.

Rahoton ya ce adadin matan da aka ci zarafin nasu ya zarce wanda ya bayyana, sai dai mafi akasarinsu sun ki bayyana kansu, saboda fargabar fuskantar tsangwama. Zalika akwai wasu matan akalla 5 da dakarun na Chadi suka yi yunkurin yinwa fyaden amma suka samu sa’ar tserewa.

Cikin watan Fabarairun da ya gabata Chadi ta aike da dakarunta dubu 1 da 200 zuwa yankunan dake kan iyakokin Nijar, Mali da kuma Burkina Faso, domin karin karfi ga sojojin Faransa dubu 5 da 100 da hadin gwiwar dakarun sauran kasashen dake yakar kungiyoyin mayaka masu alaka da Al’Qaeda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.