Rikicin kogin Nile

Dimokradiyar Congo na sasanta rikicin Masar da Habasha da kuma Sudan

Madatsar ruwan da Habasha ke ginawa da kogin Nile wanda ya haifar da rikici tsakanin ta makwabtan Masar da Sudan akai.
Madatsar ruwan da Habasha ke ginawa da kogin Nile wanda ya haifar da rikici tsakanin ta makwabtan Masar da Sudan akai. AFP/File

Ministocin Kasashen Masar da Habasha da Sudan sun fara gudanar da wani taro a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da zummar sasanta rikicin da ya biyo bayan shirin gina madatsar ruwan da Habasha keyi akan Kogin Nilu wanda ya haifar da rikici a tsakanin su.

Talla

Shugaban kasa Felix Tshisekedi dake jagorancin kungiyar kasashen Afirka ta AU ya bukaci ministocin da su bude wani sabuwar kofar da zata bada damar fahimtar juna da kuma kulla yarjejeniya a tsakanin su.

Tshisekedi ya yabawa kasashen uku saboda yadda suka yadda a sasanta barakar dake tsakanin su a Afirka maimakon zuwa kasashen duniya.

Jakadan Amurka a Congo Mike Hammer na daga cikin wadanda suka halarci bikin bude taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.