Habasha-Masar-Sudan

Habasha, Masar da Sudan na taro kan makomar gina dam a kogin Nilu

Yankin da kasar Habasha ke kokarin gina madatsar ruwa akan kogin Nilu.
Yankin da kasar Habasha ke kokarin gina madatsar ruwa akan kogin Nilu. AP - Elias Asmare

Ministocin harkokin wajen kasashen Habasha, Masar da kuma Sudan sun shiga sabon zagaye na tattaunawa kan lalauben mafitar ware-ware takaddamar da suka share shekaru suna yi, kan shirin Habasha na gina madatsar ruwa a kan kogin Nilu.

Talla

Taron da kasashen suka soma  a ranar Asabar zai shafe kwanaki uku yana gudana a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, wadda ke rike da jagorancin karba-karba na kungiyar hadin kan kasashen Afrika ta AU.

A ranar Talatar makon jiya shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi, yayi gargadin cewa shirin Habasha na gina madatsar ruwa akan kogin Nilu barazana ce babba, da za ta haifar da tashin hankali a daukacin yankuna 7 dake zagaye da kogin na Nilu wanda akalla kasashe 10 ke amfana da shi.

Ruwan kogin Nilu da ya ratsa cikin Khartoum babban birnin kasar Sudan.
Ruwan kogin Nilu da ya ratsa cikin Khartoum babban birnin kasar Sudan. AP - Sayyid Azim

Gwamnatin Habasha dai na kare shirin ta na gina madatsar ruwan da cewar zai samar da hasken wutar lantarki ga ‘yan kasar miliyan 110.

Sai dai Masar da ta dogara kan kogin Nilu da kashi wajen samun ruwan sha da noman rani na kallon gina dam din a matsayin babbar barazana. Itama dai Sudan na adawa da shirin Habasha ne, saboda barazanar da hakan ke yiwa na ta madatsun ruwan da ke amfana da kogin.

Kawo yanzu dai an shafe kusan shekaru 10 ana sa in sa tsakanin Masar da Sudan, da kuma Habasha dangane da shirinta na gina madatsar ruwan akan kogin Nilu, zalika duk yunkurin sulhun da aka yi ya gaza kawo karshen takaddamar da kasashen ke yi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.