Nijar - Algeria

Algeria ta sake tasa keyar daruruwan 'yan ci rani zuwa Nijar

Wasu 'yan Jamhuriyar Nijar dake shirin tafiya Libya ci rani.
Wasu 'yan Jamhuriyar Nijar dake shirin tafiya Libya ci rani. AP - Jerome Delay

Kasar Algeria ta sake tasa keyar 'yan asalin kasashen Afirka yankin kudu da Sahara su 678 da suka hada da mata da yara kanana zuwa gida, mutanen da tuni suka sauka isa garin Agadas da ke arewacin Jamhuriyar Nijar.

Talla

Algeria dai na zargin ‘yan ci ranin da mafi yawansu 'yan kasar Nijar ne  da shiga kasar ta barauniya hanya.

Adadin dai shi ne mafi yawa na 'yan cirani da Algeria ta maida zuwa Nijar, kamar yadda za a ji cikin rahoton wakilinmu na Agadez Umar Sani.

Rahoto kan yadda Algeria ta sake tasa keyar daruruwan 'yan ci rani zuwa Nijar
Rahoto kan yadda Algeria ta sake tasa keyar daruruwan 'yan ci rani zuwa Nijar

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI