Habasha-Tigray

Dakarunmu na yaki da 'yan tawaye a yankuna 8 na Habasha- Abiy

Firaministan Habasha Abiy Ahmed.
Firaministan Habasha Abiy Ahmed. REUTERS/Kumera Gemechu

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya bayyana cewar yanzu haka dakarun kasar sa na gudanar da yake yake a yankuna guda 8 da ke fadin kasar ciki har da yankin Tigray inda sojojin suka murkushe 'yan tawaye.

Talla

Shugaba Abiy Ahmed ya ce 'yan tawayen da aka murkushe makwanni 3 da suka gabata yanzu sun rikide sun zama 'yan sari ka noke da suka saje da manoma suna kai hare hare jifa jifa.

Firaministan ya ce sajewar su cikin jama’a ya haifar da tsaiko wajen kawar da su saboda kaucewa afkawa fararen hula.

Rundunar sojin kasar na gudanar da yaki da wasu 'yan tawayen daban a yankin Oromia wadanda aka zarga da kashe fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.