Rwanda

Faransa ta bada umurnin bada damar duba bayanan asirin dangane da kisan Rwanda

Paul Kagame Shugaban kasar Rwanda
Paul Kagame Shugaban kasar Rwanda REUTERS - JEAN BIZIMANA

Gwamnatin Faransa ta bada umurnin bude kayayyakin dake dauke da bayanan tarihin da suka shafi harkokin diflomasiyya lokacin kisan kare dangin da akayi a kasar Rwanda shekaru 27 da suka gabata.

Talla

Wadannan kayayyakin tarihin sun kunshi bayanan matakan da gwamnatin shugaba Francois Mitterand da Firaministan sa Edouard Balladur suka dauka tsakanin shekarar 1990 zuwa 1994 da aka aikata kisan kare dangin da ya gudana..

Sanarwar da gwamnatin Faransa ta gabatar yace takardun bayanan sun kunshi sakwannin telegram da bayannan sirri wadanda suke cikin abubuwan da kwamitin binciken da masana tarihi suka duba kafin gabatar da rahotan su a watan jiya ga shugaba Emmanuel Macron.

Akalla mutane 800,000 aka tabbatar da mutuwar su a kazamin tashin hankalin da aka samu tsakanin Yan kabilar Hutu da Tutsi kuma akasarin wadanda aka kashe sun fito ne daga Tutsi.

Shugaban Rwanda Paul Kagame ya yaba da matakin da gwamnatin Faransa ta dauka wanda ya ke cewa kasar ta dauki alhakin kauda kai kan da tayi lokacin kisan kiyashin da akayi, duk da yake tace babu hannun ta a ciki.

Kagame yace wannan ya zama matakin farko na samun fahimtar juna tsakanin kasashen biyu dangane da abinda ya faru lokacin tashin hankalin.

Yayin bikin tunawa da mutanen da suka mutu a rikicin da akayi yau shekaru 27 bayan tashin hankalin, shugaba Paul Kagame da uwargidan sa Jeannette sun kunna fitilar tunawa da wadanda rikicin ya ritsa da su a Kigali.

Kagame wanda tsohon shugaban Yan Tawayen Tutsi ne ya kwashe shekaru 27 yana jagorancin Rwanda.

Tashin hankalin na Rwanda ya biyo bayan kisan gillar da aka yiwa shugaban kasa Juvenal Habyarimana lokacin da aka harbo jirgin saman da yake ciki a ranar 6 ga watan Afrilun shekarar 1994.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.