Cote d’Ivoire-Gbagbo

Gbagbo da Ble Goude na iya komawa gida -Ouattara

Alassane Ouattara.Shugaban kasar Cote D'Ivoire
Alassane Ouattara.Shugaban kasar Cote D'Ivoire REUTERS/Luc Gnago/File Photo

Shugaban Cote d’Ivoire Alassane Ouattara, ya ce tsohon shugaban kasar Laurent Bagbo da kuma jagoran matasa ‘yan gani-kashe-ni da ke mara masa baya wato Charles Ble na iya komawa gida a duk lokacin da suke bukata, bayan da kotun duniya ta ICC ta wanke su daga laifufukan da ake zarginsu da aikatawa.

Talla

Shugaba Ouattara, wanda ke jagorantar taron majalisar ministocin kasar a wannan laraba, ya ce bayan dawowarsa a gida tsohon shugaba Laurent Bagbo zai ci moriyar illahirin hakkokin da doka ta ce a bai wa tsohon shugaban kasar.

A game da daukar nauyi da kuma dawainiyar tsohon shugaban da iyalansa domin komowa gida kuwa, shi ma wannan zai fito ne daga Baitul-malin kasar a cewar shugaba Ouattara.

To sai da shugaban kasar bai bayyana makomar hukuncin daurin shekaru 20 da wata kotu ta yanke wa Laurent Bagbo bayan samun sa da hannu a fashin da aka kai wa bankin kasashen yammacin Afirka na BCEAO kuwa lokacin da ake tsakiyar yakin basasar kasar ba.

 A ranar 31 ga watan jiya ne kotun ta ICC ta wanke Laurent Bagbo da kuma Charles Ble goude daga illahirin zarge-zargen da ake yi masu, matakin da ke share masu fagen komawa gida Cote d’Ivoire idan suna bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.