Chadi-Zabe

Kare hakkokin bil Adam na daga cikin ka'idojin da ya dace Chadi ta yi aiki a kai

Tsohon Minista kuma dan takara a zaben kasar Chadi Pahimi Padacket Albert
Tsohon Minista kuma dan takara a zaben kasar Chadi Pahimi Padacket Albert © Madjiasra Nako / RFI

Sakatary Majalisar Dimkin Duniya Antonio Gutteres a jiya juma’a ya kira hukumomin kasar Chadi da su mutunta dokokin kare hakkokin bil Adam.Kiran Guttersh na zuwa a jajuburin zaben Shugabancin kasar a gobe lahadi.

Talla

Kiran Gutteres na zuwa dai-dai lokacin da aka kawo karshen yakin neman zaben kasar jiya juma’a, zaben da yan adawa ke ikirarin cewa jam’iyya mai mulki ta shirya tafka magudi.

Shugaban kasar Chadi kuma dan takara Mareshal Deby
Shugaban kasar Chadi kuma dan takara Mareshal Deby © AFP - RENAUD MASBEYE BOYBEYE

Antonio Gutters ya yaba da jan aiki da kafofin yada labaren kasar ke yi a wannan lokaci da wasu daga cikin su ke fuskantar barrazana daga hukumomin kasar ta Chadi.

Shugaban kasar kuma dan takara Mareshal Idris Deby Itno da ya share shekaru 30 a kan karagar mulkin  ke sake neman wani wa’adi na shida a zaben da zai gudana  ranar lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.