Djibouti

Shugaban Djibouti ya lashe zaben kasar da kusan kashi 98

Yakin neman zaben kasar Djibouti
Yakin neman zaben kasar Djibouti © AFP - Tony Karumba

Shugaban kasar kuma dan takara  Ismaël Omar Guelleh da ya share shekaru 22 a kan karagar mulkin kasar Djibouti ya lashe zaben shugabancin kasar da kusan kashi 98 cikin dari na kuri’u da aka kada.

Talla

Akala mutane 215.000 ne hukumar zaben kasar ta tattance ,Shugaban kasar ya samu  kuri’u 167.535,Guelleh da aka Haifa a shekara ta 1947 a Dire-Dawa na kasar Habasha na daga cikin yan mazan jiya da suka taka muhimiyar rawa ta fuskar siyasar kasar Djibouti.

Shugaban kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh tareda Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh tareda Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron © AFP - Ludovic Marin

Duk zaben da aka shirya wannan kasa,Shugaban Ismail Omar Guelleh na samun sama da kashi 75 cikin dari na kuri’u.

Ko a wannan karo,yan adawa sun komaci kauracewa zaben ,wanda ya kuma ba shi damar  lashe zaben ba tareda wata matsala ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.