Benin

Yan sanda sun kama 'yan Adawa a Jamhuriyar Benin biyo bayan tarzoma

Yan sanda a Jamhuriyar Benin
Yan sanda a Jamhuriyar Benin AFP - YANICK FOLLY

A Jamhuriyar Benin akalla mutane biyu suka mutu sanadiyyar rikicin siyasa da ya kuno kai a arewacin kasar. Yayinda gwamnati ta aike da karin dakaru zuwa arewacin kasar  inda jama’a ke bukatar Shugaban kasar kuma dan takara Patrice Talon ya yi murabis.

Talla

A marecen jiya juma’a ‘yan sanda sun sake kama wasu yan adawa biyu da suka hada da Alexandre Hountonji da Josaeph Tamegnon aka kuma garzaya da su kurkuku bisa zargin da ta’adanci.

Kalo ya koma bangaren gwamnati yanzu haka ,inda wasu ke ganin cewa zai yi wuya a gudanar da zaben a gobe a wasu yankunan kasar musaman arewacin kasar sabili da tarzoma.

Kasashen Duniya na cigaba da kira ga ‘Yan Siyasar kasar don ganin sun cimma zaman lafiya a wannan lokaci na zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.