Zaben Benin

Al'ummar Benin na gudanar da zaben shugaban kasa cikin fargaba

Shugaban kasar Benin Patrice Talon lokacin da yake kada kuri'ar sa Kotonu cibiyar kasuwancin kasar, ranar 11 ga watan Afrelun shekarar 2021
Shugaban kasar Benin Patrice Talon lokacin da yake kada kuri'ar sa Kotonu cibiyar kasuwancin kasar, ranar 11 ga watan Afrelun shekarar 2021 © Patrice Talon - Twitter

Yau Lahadi 'Yan kasar Benin ke zuwa rumfunan zabe, cikin wani yanayi, sakamakon tashin hankali da aka samu, yayin da masu suka ke zargin Shugaba Patrice Talon da karkatar tsarin zaben don fifita kansa, bayan hana shugabannin ‘yan adawa takara.

Talla

Hamshakin attajirin da aka fara zaba don jagorantar kasar dake Yammacin Afirka a shekarar 2016, Talon na fuskantar abokan adawa biyu da ba a san su sosai ba, wato Alassane Soumanou da Corentin Kohoue.

Shugaban kasar Benin Patrice Talon bayan kada kuri'arsa a zaben 11 ga watan Afrelun 2021
Shugaban kasar Benin Patrice Talon bayan kada kuri'arsa a zaben 11 ga watan Afrelun 2021 © Patrice Talon - Twitter

Yawancin shugabannin jam’iyyun adawa dake gudun hijira, basu samu damar takara ba, saboda sake fasalin zabe ya hana su damar, yayin da wasu ke karkashin binciken kotu ta musamman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.