Saliyo - Ebola

Saliyo za ta yi wa ma’aikatan lafiyarta dake kan iyakar Guinea rigakafin Ebola

Zane dangane da rigakafin annobar Ebola
Zane dangane da rigakafin annobar Ebola © Dr Meddy

Gwamnatin Saliyo ta sanar da cewa za ta yi wa ma’aikatan kiwon lafiyarta allurar rigakafin cutar Ebola a yankunan da ke kusa da kan iyakarta da Guinea, inda cutar ta sake bulla a watan Janairu.

Talla

Ministan lafiyan kasar Austin Demby ya bayyana haka cikin wata sanarwa,  cewa kamfanin samar da magunguna na Amurka Johnson & Johnson zai basu allurai 640 na rigakafin cutar ta Ebola ranar Asabar da kuma dubu 3,840 a ranar Lahadi a matsayin gudummawa.

Wasu jami'an Lafiya da ke shirin tunkarar aikin rigakafin na Ebola.
Wasu jami'an Lafiya da ke shirin tunkarar aikin rigakafin na Ebola. REUTERS/Baz Ratner/File Photo

Sanarwar ta ce "lura da barkewar cutar Ebola a makwabtan Guinea, ma'aikatan lafiya dake gundumomin kan iyaka na cikin barazanar kamuwa da cutar idan har kwayar ta bazu zuwa Saliyo."

Cutar mai saurin kisa ta sake bayyana a Guinea a cikin watan Janairu, abinda yasa ake daukar makan ganin cutar batayi illa kamar wadda tayi a shekarar 2013 zuwa 2016 a Yammacin Afirka, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 11,300 a Guinea da Liberiya da kuma Saliyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.