Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Sojojin Demokradiyyar Congo sun kashe mayakan sa kai biyar

Sojan Congo da na Majalisar Dinkin Duniya a wani yanki da yan tawaye suka kai hari a congo
Sojan Congo da na Majalisar Dinkin Duniya a wani yanki da yan tawaye suka kai hari a congo ALEXIS HUGUET AFP

Sojojin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo sun sanar da kashe mayakan sa kai biyar, bayan wani kazamin fada da sukayi  a yankin gabashin kasar mai fama da rikici.

Talla

Cikin sanarwa da kakakin rundunar sojin kasar, Kaftin Diaudonne kasereka ya fitar, tace Mayakan sa kai sun kai hari ne wani sansanin sojoji kusa da Minembwe a gabashin tuddai.

Sanarwar tace, an dauki tsawon ranar Juma'a, ana gwabzawa tsakanin mayakan da sojoji, kuma ya zuwa lokacin fitar da sanarwar, adadin mayaka biyar aka kashe.

Rundunar Sojojin ta yi kira ga mazauna yankin da suka tsere su koma gidajensu, tana mai cewa yanzu haka sun shawo kan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.