Burkina-Compaore

Blaise Compaore na Burkina zai gurfana gaban kotu kan kisan Thomas Sankara

Tsohon shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore.
Tsohon shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore. Ahmed OUOBA / AFP

Hukumomin Burkina Faso sun yanke hukuncin gurfanar da tsohon shugaban kasar Blaise Compaore a gaban kotu saboda zargin da ake masa na kashe wanda ya gada shugaba Thomas Sankara a juyin mulkin da ya masa cikin shekarar 1987.

Talla

Lauyan marigayi Sankara Guy Herve Kam da ke sanar da matakin ya ce an shigar da kara a gaban kotun soji da ke Ouagadougou bayan da aka tabbatar da tuhumar akan Compaore da wasu mutane shekaru 34 bayan kisan gillar.

Kam ya ce ana tuhumar Compaore da wasu mutane 13 da laifin cin amanar kasa wadda ta kaiga kisa da kuma kitsa kisan da kuma boye gawarwaki.

Lauyan ya ce lokaci ya yi na tabbatar da gaskiya, kuma ana iya fara shari’ar wadda yanzu haka ake dakon mai gabatar da kara na soji ya sanya ranar fara ta.

Cikin wadanda ake zargi har da Janar Gilbert Diendere, wani tsohon na hannun daman Compaore kuma tsohon kwamandan dakarun da ke tsaron fadar shugaban kasa lokacin da aka yi juyin mulkin, wanda yanzu haka ya ke cin sarkar shekaru 20 saboda kitsa juyin mulkin da soji suka yi a shekarar 2015.

Lauyan ya ce daga cikin wadanda ake tuhuma wasu sun riga sun mutu, yayin da lauyan Diendere, Mathieu Some ya ce duk da ya ke ba a sanya ranar fara shai’ar ba, ana iya fara ta a kowanne lokaci.

Tsohon shugaban kasa Thomas Sankara ya gudanar da juyin mulki a shekarar 1983 amma sai aka kasha shi a ranar 15 ga watan Oktobar shekarar 1987 lokacin yana da shekaru 37 a juyin mulkin da Compaore ya jagoranta kafin shima a kifar da gwamnatin sa a shekarar 2014 bayan ya kwashe shekaru 27 a karagar mulki.

A watan Maris na shekarar 2016 kotu ta bada sammacin kamo shi a Cote d’Ivoire inda ya samu mafaka tun bayan kifar da gwamnatin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.