Benin-Zabe

Shugaba Patrice Tallon ya sake lashe zaben Benin a karo na biyu

Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon bayan lashe zabe da gagarumin rinjaye.
Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon bayan lashe zabe da gagarumin rinjaye. Sia KAMBOU / AFP

Hukumar zabe a Jamhuriyar Benin ta bayyana shugaba Patrice Tallon a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da akayi a karshen mako da kasha 86 na kuri’un da aka kada, abinda zai bashi damar yin wa’adi na biyu.

Talla

Hukumar zaben Jamhuriyar Benin ta ce shugaba Patrice Tallon ya samu kashi 86 na kuri’un da aka kada a fafatawar da suka yi da wasu 'yan takara guda biyu da suka hada da Alassane Soumanou da ya samu kashi 11.29 sai kuma Corentin Kohoue da ya samu kashi 2.25.

Kungiyoyin masu sanya ido kann zaben guda 3 sun bayyana rashin fitowar mutane sosai domin kada kuri’a sakamakon janyewar wasu 'yan adawa da suka zargi shugaba Tallon da kama karya.

Hukumar zabe ta ce kashi 50.17 na masu rajistar kuri’u ne suka shiga zaben, abinda ya bai wa tsohon dillalin auduga Tallon nasarar cigaba da zama a karagar mulki.

Daya daga kungiyoyin fararen hular da suka sanya ido a zaben sun yi zargi tirsasawa masu kada kuri’u da sayen kuri’u da kuam yi wasu barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.