Chadi-Ta'addanci

Sojin Chadi sun fatattaki 'yan tawayen da suka farwa yankin Tibesti

Wasu dakarun Sojin Chadi da ke yaki da ta'addanci a Sahel.
Wasu dakarun Sojin Chadi da ke yaki da ta'addanci a Sahel. AFP PHOTO / ALI KAYA

Gwamnatin Chadi ta sanar da nasarar shawo kan rikicin da ya barke a yankin tsaunukan Tibesti mai makwabtaka da birnin N’Djamena kwana guda bayan zaben kasar da ake sa ran shugaba Idris Deby ya ci gaba da jagoranci a karo na 6.

Talla

Sanarwar da kakakin gwamnatin Chadi Cherif Mahamat Zene ya fitar, ta ce dakarun Sojin kasar sun fatattaki ‘yan tawayen da suka farwa garin Zouarke na yankin Tibesti mai tazarar kilomita dubu guda da arewacin N’Djamena babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce da misalin karfe 6 na yammacin Lahadin da ta gabata ne ‘yan tawayen dauke da manyan makamai haye da motocin yaki daga Libya suka farwa yankin wanda ya tayar da hanklin jama’a.

Sai dai sanarwar gwamnatin ta bakin Cherif Zene ta ce babu sauran tashin hankali a yankin bayan da dakarun Sojin kasar suka fatattaki ‘yan tawayen tare da fitar da su daga kasar.

Yankin na tsaunukan Tibesti da ke gab da iyakar kasar da Libya na fuskantar tashe-tashen hankula da hare-haren mayakan ‘yan tawaye wanda ya kai ga hare-haren Sojin Faransa a farkon 2019 da ya kai ga samun sassaucin rikicin.

Ko a shekarar 2008 gungun ‘yan tawayen sai da ya kai ga kofar fadar shugaban kasar na Chadi amma kuma dakarun Soji suka fatattake su da goyon bayan Sojin Faransa.

Kakakin rundunar Sojin Chadi Azem Bermandoa Agouna ya ce tuni suka dauki matakin fatattakar mayakan ‘yan tawayen don kawo karshen barazanar ga tsaron kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.