Burkina Faso-Sankara

Darasin da shugabannin Afrika suka dauka a kisan Sankara

Marigayi  Thomas Sankara
Marigayi Thomas Sankara William F. Campbell/Time & Life Pictures/Getty Images

Hukumomin Burkina Faso sun yanke hukuncin gurfanar da tsohon shugaban kasar kasa Blaise Compaore a gaban kotu saboda zargin da ake masa na kashe wanda ya gada shugaba Thomas Sankara a juyin mulkin da ya yi masa a shekarar 1987, yayin da masana siyasa ke cewa, lallai akwai darasin da Afrika ta dauka a kisan marigayin

Talla

A yayin zantawarsa da sashen Hausa na RFI, Farfesa Usman Mohammed, masanin siyasar Afrika da ke Jami'ar Baze a Abuja ya bayyana cewa, ko babu komai, tuhumar da ake yi wa makashinsa a yanzu, ta isa ta zama babban darasi ga shugabannin Afrika, lura da cewa kusan shekaru 40 kenan da aikata laifin, amma har yanzu zancen bai kare ba.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da Bashir Ibrahim Idris ya yi da Farfesa Usman Mohammed kan wannan batu.

 

Hira da Farfesa Usman Mohammed kan kisan Sankara

 

Dole ne shugabannin Afrika su sani, za a tuhume su akan juyin mulkin da suka yi a baya, idan ta taso ma, sai an tuhume su akan me ya sa suka yi, sannan kuma tarihi ba zai taba yafe musu ba saboda mutanen da suka kashe da kuma jefa al'ummarsu cikin ukuba. Inji Farfesa Mohammed.

Yanzu haka kotun soji da ke birnin Ouagadougou na tuhumar Campore da wasu mukarrabansa 13 da yin zagon kasa ga tsaron kasa da kisan kai da kuma boye gawarwakin jama'a kamar yadda lauyan Sankara, Guy Herve Kam ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.