Faransa-Barkhane

Sai da taimakon rundunar Barkhane tsaro zai tabbata a Sahel- rahoto

Dakarun Sojin Faransa da ke cikin rundunar Barkhane mai yaki da ayyukan ta'addanci a kasashen yankin Sahel.
Dakarun Sojin Faransa da ke cikin rundunar Barkhane mai yaki da ayyukan ta'addanci a kasashen yankin Sahel. REUTERS/Benoit Tessier

Wani rahotan Majalisar dokokin Faransa ya ce babu yadda za a tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel ba tare da gudumawar rundunar sojin Barkhane da ke taimakawa hukumomin yankin wajen yaki da yan ta’adda ba.

Talla

Rahotan binciken da kwamitin tsaron majalisar ya gudanar ya ce duk da 'yan matsalolin da ake fuskanta, rundunar Barkhane za ta ci gaba da tinkarar 'yan ta’addar da ke yankin na Sahel domin tabbatar da zaman lafiya.

Kwamitin ya ce a halin da ake ciki yau, babu wata hanyar murkushe 'yan ta’addan da suka mamaye wannan yanki ba tare da taimakon wannan runduna ba.

Rahotan ya ce samun dawamammen zaman lafiya a yankin Sahel zai dauki shekaru da dama kuma martabar Faransa ita ce bada gudumawa wajen cigaba da tinkarar wadannan yan ta’adda kamar yadda ake bukata.

Kasar Faransa ta girke sojojin ta dubu 5 da 100 a yankin domin yaki da 'yan ta’addan da ke alaka da kungiyar Al Qaeda da IS.

A taron shugabannin kasashen G5 Sahel da aka yi a watan Fabarairu, shugaba Emmanuel Macron ya ce baya tunanin rage yawan sojin da ke yankin cikin gaggawa har sai an samu nasara kan kungiyoyin yan ta’addan da ke yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.