Malawi-Corona

Malawi za ta lallata alluran rigakafin corona dubu 16 da ta karba daga AU

Gwamnatin kasar ta ce za ta dauki matakin lalata alluran ne don baiwa jama'arta kariya.
Gwamnatin kasar ta ce za ta dauki matakin lalata alluran ne don baiwa jama'arta kariya. © AFP - Ebrahim Hamid

Gwamnatin kasar Malawi ta ce za ta lalata alluran rigakafin coronavirus dubu 16 da ta karba a matsayin agaji daga kungiyar kasashen Afirka ta AU saboda lalacewar da suka yi.

Talla

Sakataren lafiyar kasar Charles Mwansambo ya ce sun dauki matakin ne domin kare lafiyar jama’ar kasar wajen kaucewa amfani da gurbataccen magani.

Malawi ta kaddamar da rigakafin cutar corona a watan jiya da zummar ganin ta yiwa akalla mutane miliyan 11 ko kuma kashi 60 na jama’ar ta allurar nan da karshen wannan shekara, sai dai matakin lalacewar wasu daga cikin alluran rigakafin ka iya haddasa mata cikasa a yunkurin.

Galibin kasashen Afrika sun dogara da shirin Covax ne wajen wadata al'ummominsu da alluran rigakafin na coronavirus ko da ya ke itama kungiyar AU na kokarin samar musu da wani kaso na alluran don gaggauta fatattakar cutar daga Nahiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.