Benin

Talon ya sha alwashin hukunta masu hannu a haddasa rikicin kasar

Shugaban Jamhuriyyar Benin Patrice Talon.
Shugaban Jamhuriyyar Benin Patrice Talon. AFP/File

A Jamhuriyar Benin, Shugaban kasar Patrice Talon ya sha alwashin hukunta masu hannu a tarzomar da ta barke a jajiberan zaben shugaban kasa na ranar 11 ga watan Afrilu.Shugaba Talon na wannan batu ne a ziyarar da ya kaiwa Sojojin da suka samu rauni a tarzomar a wani asibitin Soji da ke birnin Kwatanu.

Talla

Kwana daya bayan da hukumar zaben Jamhuriyar Benin ta bayyana shugaba Patrice Talon a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da kusan kashi 86 na kuri’un da aka kada, shugaban ya ziyarci wasu daga ckin jami’an tsaron kasar da suka samu rauni a arewacin kasar 'yan kwanaki bayan da aka fuskanci tashin hankali.

Yayinda ya ziyarci sojojin a asibitin Soji da ke birnin kwatanu, Patrice Talon ya tabbatar musu cewa gwamnati za ta yi iya kokarin ta na ganin sun samu kulawar da ta kamata, yayinda ya sha zakulo wadanda ke da hannu a rikicin bayan kammala binciken da ya ce yanzu haka an faro don gano musabbabi da kuma masu hannu a daukar nauyinsa.

Shugaba Talon ya ce mutanen da suka afkawa Sojojin na dauke da makaman yaki wanda ya bayyana a matsayin babbar barazana.

Akalla jami'an tsaron kasar 28 suka jikkata a farmakin wanda wasu mutane dauke da muggan makamai suka afka musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.