Kamaru - Coronavirus

Kamaru: Jami’an lafiya sun ki yadda da rigakafin Korona na Sinopharm

Jami'an lafiya a asibitin Quinquinie  dake birnin Douala na kasar Kamaru, yayin shirin fara aikin duba masu fama da cutar Korona.
Jami'an lafiya a asibitin Quinquinie dake birnin Douala na kasar Kamaru, yayin shirin fara aikin duba masu fama da cutar Korona. © REUTERS/Josiane Kouagheu

Jami’an kiwon lafiya da dama a Kamaru sun ki amincewa a yi musu allurar rigakafin kariya daga cutar covid-19 samfurin Sinopharm, wanda China ta bai wa kasar.

Talla

Daga cikin allurai dubu 200 da kasar China ta baiwa Kamaru domin yi wa jama’a rigakafin wannan cuta, an rarraba allurai dubu 14 da 700 a cikin cibiyoyin kiwon lafiya 20 dake yankin yammacin kasar.

Tun ranar 13 ga wannan wata na Afrilu ne aka kaddamar da rigakafin a garin Bafoussam dake matsayin fadar gwamnatin yankin, kuma daga cikin wadanda aka yiwa allurar har da gwamnan lardin Mista Awa Fonka da sauran manyan jami’an gwamnati.

Sai dai duk da cewa su ne ya kamata a yi wa rigakafin saboda kasancewarsu masu mu’amala kai-tsaye da marasa lafiya, jami’an kiwon lafiya a wannan yanki sun ki amincewa a yi masu wannan allura, lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin al’umma dangane da maganin Sinapharm na kasar China.

Daga cikin wadanda suka ki amincewa a yi masu wannan allura har da Dakta Jules Hilaire Focka-Focka, wanda kwararren likita ne a asibitin Bafoussam, kuma shugaban majalisar lardin Yammacin kasar, wanda duk da cewa kimanin watanni biyu da suka gabata an gano ya harbu da cutar covid-19, amma ya ce ba zai yarda a yi masa wannan allura ba sai nan da watanni shiga masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.