Benin-Zabe

Kotu ta amince da nasarar Talon a zaben Benin

Patrice Talon
Patrice Talon © AFP/Seyllou

Kotun Fasalta Kundin Tsarin mulki da ke Jamhuriyar Benin ta amince da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a karshen mako wanda ya bai wa Patrice Talon nasarar samun wa’adi na biyu.

Talla

Matsayin kotun na zuwa ne jim kadan kafin yi wa abokin takarar shugaban Joel Aivo da aka haramta wa shiga zaben tambayoyi dangane da tashin hankalin da aka samu a kasar.

Shugaban Kotun Joseph Djogbenou ya ce, sun amince da sakamakon na wucen-gadi, inda suka bukaci masu korafi da su gabatar nan da kwanaki 5 masu zuwa.

Hukumar zabe ta bayyana cewar shugaba Talon ya samu sama da kashi 86 na kuri’un da aka kada a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.