Tunisia - 'Yan Ci Rani

'Yan ci rani 41 sun mutu a gabar ruwan Tunusia

Gawarwakin wasu 'yan ci rani da aka tsamo daga gabar ruwan Tunisia.
Gawarwakin wasu 'yan ci rani da aka tsamo daga gabar ruwan Tunisia. AP - Houssem Zouari

Rahotanni daga kaasr Tunisia sun ce akalla mutane 41 suka mutu lokacin da kwale kwalen dake dauke da baki ya kife a kusa da gabar ruwan Tunisia.

Talla

Hukumar kula da kauran baki ta Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar dake kula da kauran baki da ta duniya sun ce an ceto mutane 3 da ran su, yayin da aka tsamo gawarwakin mutane 41 cikin su harda karamin yaro guda.

Rahotanni sun ce an dakatar da neman sauran gawarwaki a ruwan saboda gurbacewar yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.